Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ya san cewa Allah ya amsa addu’arsa ta sake ci gaba da jagorantar ƙasar bayan kammala wa’adinsa na farko a shekarar 2027.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin da yake bayyana irin addu’o’in da ya yi a lokacin da ya samu damar shiga cikin ɗakin Ka’aba mai alfarma a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya, yayin gudanar da aikin Umrah.
Tinubu ya ce ya roƙi Allah Ya ba shi hikima da juriyar ci gaba da yi wa al’ummar Najeriya hidima, yana mai cewa yana da yakinin Allah Ya amsa wannan addu’a tasa.
Ya kuma tuna cewa ya yi irin wannan addu’a kafin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, inda ya roƙi Allah Ya albarkaci tafiyarsa ta Umrah, tare da alƙawarin dawowa domin yin godiya idan addu’ar ta cika.
Shugaban ya ƙara da cewa mulki da ikon mallakar duniya na Allah ne, wanda yake ba wa wanda Ya so, kuma yana karɓewa daga wanda Ya so, don haka wajibi ne shugabanni su yi amfani da amanar mulki cikin gaskiya da adalci.
Ya kuma jaddada cewa ƙudurinsa na ci gaba da ayyukan raya Najeriya ya ƙara ƙarfi, tare da alƙawarin mayar da hankali wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da makoma mai kyau ga matasa.

