Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta kalubalanci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya gabatar da sahihan hujjoji kan zargin da ya yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na katsalandan a harkokin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), domin hana amincewa da ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar (NDC) a zaɓen 2027.
APC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Ofishin mai magana da yawun kwamatin yaƙin neman Zaɓen Shugaban Ƙasa da Gwamnan Jihar Kano na II wato Hon.Muhammadu Sunusi Kiru ya fitar a ranar 2 ga Nuwamba, 2026, inda ta kuma yi martani kan ikirarin Kwankwaso cewa Gwamna Abba yana nadamar ficewa daga tafiyar Kwankwasiyya da komawa APC.
A cewar sanarwar, zarge-zargen da tsohon gwamnan Kano ya yi na buƙatar hujjoji na zahiri, maimakon jingina su ga sauyin matsayar siyasa da rashin jituwa tsakanin tsoffin abokan siyasa.
Jam’iyyar ta kuma tuna wa Kwankwaso cewa a zaɓen shekarar 2019, lokacin da Gwamna Abba yake takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin jam’iyyar PDP tare da goyon bayansa, takarar ta fuskanci ƙalubalen shari’a.
Sanarwar ta ce Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci kan takarar Abba a ranar 4 ga Maris, 2019, amma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin a ranar 8 ga Maris, kwana guda kafin zaɓen gwamnan jihar.
Haka kuma, jam’iyyar ta bayyana cewa matsalolin tantance ‘yan takara da takardun neman zaɓe ba su tsaya a Jihar Kano kaɗai ba. Ta yi nuni da bayanan da ta ce INEC ta fitar, inda ta bayyana cewa hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 69 daga jam’iyyun siyasa 12 a jihohi 26, ta amince da 41, yayin da ta ƙi amincewa da 28.
Ta ƙara da cewa wasu jihohi kamar Ogun da Gombe ma sun fuskanci irin waɗannan matsaloli, don haka bai dace a ɗora wa Gwamna Abba alhakin dukkan matsalolin da suka shafi zaɓe ba.
Dangane da takarar NDC a Kano kuwa, APC ta ce jerin sunayen ‘yan takarar gwamna da INEC ta sabunta a ranar 31 ga Oktoba, 2026, ya nuna akwai takunkumin da ya shafi tikitin jam’iyyar sakamakon umarnin kotu.
A ƙarshe, APC ta jaddada goyon bayanta ga ‘yancin INEC, bin umarnin kotuna da kuma warware duk wata takaddama da ta shafi zaɓe ta hanyoyin da doka ta tanada.
Ta kuma yi kira ga Kwankwaso da ya guji maye gurbin hujjoji da bambancin ra’ayin siyasa, tana mai cewa ya kamata a gudanar da fafatawar siyasa cikin mutunta juna da kuma kare martabar hukumomin dimokuraɗiyya.

