An buɗe cikin ɗakin Ka’aba mai alfarma ga Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a yayin ziyarar ibadar Umrah da yake gudanarwa a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.
Shugaba Tinubu ya samu damar shiga cikin ɗakin Ka’aba a ranar Lahadi, inda ya samu tarba daga Sheikh Dahlulah Muthawal na Masallacin Harami, wanda ya kasance cikin waɗanda suka raka shi yayin wannan ziyara.
TST Hausa ta rawaito cewa Tinubu ya taba yin umarah a Nuwamban 2023 amma babu tabbas ko an bude masa Ka’aba.
Haka kuma, jami’in kula da harkokin fadar shugaban ƙasa, Ahmad Zafeer, na daga cikin waɗanda suka halarci wannan ziyara.
Shugaban ƙasar ya isa Saudiyya ne domin gudanar da ibadar Umrah, inda ya kuma bayyana cewa ya yi addu’o’i ga Allah domin samun zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a Najeriya.
A yayin ziyarar tasa, Tinubu ya roƙi Allah Ya ba shugabannin Najeriya hikima wajen gudanar da mulki, tare da kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Haka kuma, a wani taron cin abincin dare da ya gudanar da tawagarsa a ranar Lahadi, shugaban ya yi addu’ar Allah Ya mayar da bambancin addini, ƙabila da al’adu da ke tsakanin ‘yan Najeriya zuwa hanyar samun haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Ya ce: “Allah Ya albarkaci Najeriya, Ya mayar da bambancin da ke tsakaninmu zuwa arziki da wadata ga ƙasarmu.”
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ya gudanar da ibadar Umrah ne tun da sanyin safiyar Juma’a, inda ya zagaya Ka’aba tare da yin addu’o’i domin Najeriya da al’ummarta.

