Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke cewa wasu matasa sun jefi ayarin motocin shugaban ƙasa bayan ya halarci sallar Juma’a a Masallacin Shagari da ke Area 1, Abuja.
Babban hadimin shugaban O’tega Ogra, wanda shi ne Babban Mataimaki na Musamman ga shugaban ƙasa kan hulɗar kafafen sada zumunta na zamani, ya bayyana bidiyon da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta a matsayin mai ruɗarwa.
Cece-kuce kan lamarin ya biyo bayan wani bidiyo da jigon ADC, Dino Melaye, ya wallafa, wanda ya nuna wasu matasa suna jifan ayarin motocin da ake zargin na shugaban ƙasa ne.
A cikin bidiyon, an ji matasan suna cewa “Ba ma yi, ba ma so”, wadda ke nuna rashin goyon bayansu ga shugaban ƙasa.
A martaninsa, Ogra ya wallafa wani bidiyo da ya ce shine na gaskiya wanda ke nuna Tinubu yana fita daga masallacin cikin nutsuwa bayan kammala sallar Juma’a.
Bidiyon ya nuna shugaban ƙasa sanye da fararen kaya da hula baƙa, yana daga wa magoya bayansa hannu tare da karɓar gaisuwarsu yayin da yake nufar motarsa.
Ogra ya yi zargin cewa ɓangaren adawa sun ƙirƙiri Bidiyon karya domin haifar da rikicin siyasa.
Sai dai bidiyon da Ogra ya wallafa bai tabbatar da kansa ko abin da Melaye ya nuna bai faru a wani wuri dabam a kan hanyar da ayarin motocin shugaban ƙasar ya bi ba.
Wannan ya sa batun ya ci gaba da tayar da muhawara a kafafen sada zumunta, yayin da fadar shugaban ƙasa ke musanta cewa an kai wa Tinubu hari a lokacin ziyararsa masallacin.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan tashe tashen hankalin siyasa gabanin zaɓen 2027

