Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta musanta rahotannin da ke cewa ta cire sunayen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, daga shafinta na jerin sunayen masu neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ne ya bayyana hakan, inda ya ce hukumar ba ta karɓi sahihin kwafin hukuncin kotun da ya soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark ba.
Ya ƙara da cewa hukumar ba ta zauna domin tattauna hukuncin ba, don haka babu wani mataki da ta ɗauka kan sunayen ‘yan takarar.
Haruna ya bayyana cewa binciken da aka gudanar a shafin hukumar ya nuna cewa har yanzu sunayen Atiku Abubakar da abokin takararsa, Rotimi Amaechi, suna nan.
Wannan na zuwa ne bayan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark, tare da rushe matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen fidda gwani da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.

