Shugaban Majalisar Malamai ta Arewacin Najeriya, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa mazajen da ba sa son ganin matansu suna aikata kuskure, kuma suke saurin fusata idan suka yi abin da bai dace ba, na daga cikin waɗanda suke matuƙar ƙaunar matansu.
Sheikh Khalil ya ce namijin da yake ƙaunar matarsa da gaske ba ya jin daɗin ganin ta aikata abin da zai iya jawo mata matsala ko kuma ya sa ta kauce wa kyakkyawar tarbiyya.
Ya bayyana hakan ne a dakin taro na Dantata dake gidan marigayi malam Aminu Kano dake Gwammaja lokacin wani taro dake da alaka da zamantakewar aure da wasu mahimman batutuwa.
A cewarsa, irin wannan namiji yana son ganin matarsa tana tafiya a kan turbar da ta dace, kuma tana guje wa abubuwan da ba su dace ba.
Malamin ya ƙara da cewa wasu mazaje kan nuna fushinsu ne idan suka ga matansu sun aikata kuskure, ba wai don sun daina ƙaunarsu ba, sai dai saboda ba sa son ganin mutanen da suke ƙauna suna aikata abubuwan da ba su dace ba.
Sai dai ya nuna cewa abin takaici shi ne, mata da dama ba sa fahimtar irin wannan hali, inda wasu kan ɗauki saurin fushin mazajensu a matsayin rashin ƙauna, alhali kuwa a fahimtarsa, hakan na iya kasancewa wata alama ce ta damuwa da kulawarsu.
Ya kamata ma’aurata su fahimci juna, su riƙa tattauna matsalolinsu cikin hikima, haƙuri da mutunta juna, domin zaman aure mai ɗorewa yana buƙatar fahimtar juna da kyakkyawar mu’amala.

