Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya zargi ƙungiyar Kwankwasiyya da ƙirƙirar labarin kai wa ayarin motocin tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, hari a ƙaramar hukumar Bichi, domin neman tausayin jama’a.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya nuna shakku kan rahoton harin, yana mai cewa babu hotuna ko bidiyoyin da suka tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai kakakin ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Kwamared Ibrahim Garba Shu’aibu, ya tabbatar da harin, inda ya ce wasu matasa sun tare hanyar tawagar kamfen ɗin kafin su far musu da duwatsu da wasu makamai.
Ya ce tawagar ta ziyarci ƙananan hukumomi shida da suka haɗa da Tofa, Rimin Gado, Kabo, Gwarzo, Shanono da Bagwai ba tare da samun wata matsala ba, kafin tafiyarsu zuwa Bichi.
A cewarsa, bayan isa Bichi ne suka lura da alamun jifan motocinsu, kafin wasu fusatattun matasa ɗauke da makamai su fito suka far wa ayarin motocin.
Kakakin ya yi zargin cewa maharan sun jikkata wasu mambobin tawagar tare da lalata motoci da dama, yana mai cewa da kansa ya ga motoci kusan bakwai da aka lalata.
A nasa martanin, kwamishinan ya kuma yi tsokaci kan yadda jam’iyyar NDC ta gudanar da ziyara a ƙananan hukumomi bakwai cikin yini guda, yana mai cewa masu fahimtar siyasar Kano za su san ma’anar hakan.
Wannan takaddama na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun zafafa rikicin siyasa a Kano, inda magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da na tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ke musayar zarge-zarge kan lamarin da ya faru a Bichi.

