Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya gargadi ’yan siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnati da su guji ɗaukar nauyin aikin Hajji ko ziyara zuwa ƙasa mai tsarki da kuɗaɗen da aka samu ta hanyar almundahana ko cin hanci.
Sultan ya bayyana hakan ne a Abuja, a yayin buɗe taron masu ruwa da tsaki na Majalisar Ƙasa ta Haɗin Kan Addinai, NIREC, mai taken “Shared Sacred Flourishing in Nigeria”.
Ya ce ba daidai ba ne mutum ya saci kuɗi sannan ya yi amfani da su wajen ɗaukar nauyin mutane zuwa Makka ko Kudus, yana mai cewa Allah ba ya karɓar ibadar da aka gudanar da dukiyar haram.
Ya kuma yi kira ga shugabannin addinai da su ƙara ba da gudunmawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, tare da haɗin gwiwa da hukumomin yaƙi da rashawa. Sultan ya ce hukumar EFCC ta kamata ta gudanar da aikinta ba tare da tsoma bakin siyasa ba, kuma duk wanda ya aikata laifi ya fuskanci hukunci ba tare da la’akari da addininsa ko matsayinsa ba.
Sarkin Musulmin ya kuma yi kira ga malaman addinai da su riƙa yin taka-tsantsan da kalaman da suke yi a kan mimbari, musamman a lokutan zaɓe, yana mai cewa ya kamata su riƙa addu’a ga shugabannin ƙasa maimakon amfani da wuraren ibada wajen rura rikici ko rarrabuwar kawuna.

