Daga Sani Dan Bala Gwarzo
Tsohon kwamishinan kasafi da tsare tsare,na Kano kuma tsohon shugaban kwamitin tasarrafi da rabon filaye a lokacin gwamnatin Dr Abdullahi Umar ganduje,Hon Ibrahim Dan Azumi Gwarzo yace APC bata bukatar Kwankwaso a cikinta.
Ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a birnin Kano.
,Dan Azumi gwarzo yace jam’iyar APC bata bukatar irin su kwankwaso ahalin yanzu, domin duk jam’iyar da ya shiga Sai ya haddasa rigima.
Gwarzo sannan yace jam’iyar APC a yanzu kanshin Dan goma take kasancewar yadda ake ta tururuwar wajen shigartq.
Daga nan ya yi kira ga al’umma musamman yayan jam’iyar APC dasu cigaba da bawa shugaban kasa hadin Kai da goyon baya domin cigaba da aiyukan raya kasa.