Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da karin shekarun ritayar aiki ga likitoci da sauran ma’aikatan lafiya daga shekarun haihuwa 60 zuwa 65.
Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), Dr Mannir Bature ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Legas.
Dr Bature ya kara dacewa ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Pate, shine ya gabatar da amincewar da Shugaban kasa yayi a hukumance ga Kungiyar tasu.
Yace a yanzu haka an aike da batun zuwa ofishin kula da ma’aikata na gwamnatin tarayya domin yin gyare gyare a cikin ayyukan likitocin Najeriya da ma’aikatan lafiya.
Ya ce Farfesa Pate ne ya gabatar da wannan matsayar a yayin wani babban taro da shugaban Kungiyar likitoci ta kasa NMA, Farfesa Bala Audu, da masu ruwa da tsaki a fannin lafiya.
Bature ya ce taron ya kuma samu halartar shugabannin kungiyar likitan hakora ta Najeriya (MDCAN), da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa da Kungiyar ma’aikatan lafiya ta Najeriya.
Kamfanin Dillalan labarai na kasa NAN ya rawaito cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da karin wa’adin aikin likitocin da ma’aikatan lafiya a Najeriya ne saboda mahimmacin aikinsu ga jama’a da kuma kwarewarsu a kowanne bangare.
Daga nan Ministan ya godewa dukannin masu ruwa da tsaki da likitoci abisa juriyar da suka nuna har wannan shiri na karin shekaru a aikinsu ya tabbata.

