Cibiyar kasuwanci da zuba jari da masana’antu ta Kaduna (KADCCIMA) ta bayyana aniyarta na hadin guiwa da rukunin Kamfanonin Dangote domin inganta kasuwanci tsakanin bangarorin biyu.
Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, Darakta Janar na kungiyar, Alhaji Usman Saulawa, ya bayyana Kamfanonin rukunin Dangote a matsayin kamfanin da ke taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
Ya bayyana cewa, kamfanin ba wai kawai ya yi tasiri mai kyau ga ‘yan kasuwa a jihar Kaduna ba, harma da bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban Nijeriya, dama duniya baki daya.
Ya ce kasashe biyar ne ke halartar bikin baje kolin mai taken Inganta Masana’antu, da Ciniki da Noma ta hanyar amfani da Na’ura mai kwakwalwa.
Darakta Janar ya yaba da hadin gwiwa tsakanin KADCCIMA da kamfanin Dangote, inda ya yabawa Aliko Dangote, saboda gudun mowarsa wajen ciyar da tattalin arziki gaba.
Darakta Janar din ya ce kimanin kamfanoni 300 da suka kasance kanana da matsakaitan suke halartar baje kolin

