Shugaban kasar Amurika Donald Trump ya zargi tsohon shugaban kasar Joe Biden da hannu wajen haddasa tashin goron zabi na farashin kwai a kasar.
Ya bayyana hakan ne a jawabinsa a wajen taron hadin gwiwa na majalisar dokokin Amurika da ya guda a daren Talata a fadar white house.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da hauhawar farashin kwai ya zama ruwan dare a biranan Amurika musamman a baya-bayan nan.
Trump, wanda ya yiwa Amurikawa alkawarin cewa zai kawo karshen tashin farashin Kwai a kasar idan ya koma mulki,yace tsohon shugaban kasar Biden shine ya haddasa tsadar Kwan kaji ba tare da daukar mataki ba.
“Kamar yadda kuka sani, mun gaji wannan tsada, daga gwamnatin da ta gabata, ga kuma masifar matsalar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki,da muka tarar, amma kuyi hakuri komai zau wuce”, in ji Trump.
TST Hausa ta rawaito cewa Trump din yace farashin kwai ya yi tashin gwauron zabi a karkashin gwamnatin Biden ne lokacin da ya bada umarnin kashe miliyoyin kaji saboda fargabar barkewar cutar murar tsuntsaye.
Trump yace daga nan ba’a dauki wani mataki na zahiri ba ,domin maye gurbin hasarar da akayi na tsuntsayen da aka kashe ba ,wanda daga nan ne farashin kwai ya tashi a Amurika.
Rahotanni nacewa a karshen watan Janairun shekarar 2025 ana sayar da dozin din Kwai (guda 12) akan Dala 4.95 Inda a kuɗin Najeriya ya kama sama da naira 7,500
A kuɗin Najeriya ana sayar da duk kwai guda 1 akan naira 625

