Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin kara lokacin rufe kasuwanni a Kano saboda azumin Ramadan na bana.
Shugaban hukumar kula da kasuwar sabon Gari a jihar Kano Alhaji Abdul-Bashir Husain shine ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai a ofishinsa.
TST Hausa ta rawaito cewa kasuwannin da karin lokacin rufewar ya shafa sun hada da kasuwar Sabon Gari da Singa da kasuwar Galadima.
Alhaji Abdul-Bashir yace gwamnatin Kano ta kara lokacin rufe kasuwanni ne domin jama’a su samu damar yin hada hada yadda kamata.
“Mun kara mintuna 30 a kowacce rana na rufe kasuwannin guda uku saboda albarkacin watan azumin Ramadan”Inji Abdul-Bashir.
Yace a yanzu maimakon karfe 6 da ake rufe kasuwanni, za’a koma karfe 6:30 na yamma .
Shugaban hukumar kula da kasuwar ta Sabon Gari yace saboda sauyin yanayi,rana bata faduwa da wuri , shiyasa aka kara lokacin rufe kasuwanni,Amma za’a koma tsarin baya idan azumi ya wuce.
Abdul-Bashir B Husain ya kuma shida cewa bude kasuwanni guda uku wato karfe 8 na safe na nan daram.
Ya roki yan kasuwar da su baiwa gwamnati hadin kai wajen tabbatar da ana bude kasuwannin da rufe su a lokacin da aka tsara

