Gwamnatin Kano ta sanar da ranar komawa makarantun Furamare da Sakandare a Kano domin cigaba da karatun zango na uku na shekarar 2024 zuwa 2025.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai da wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta Kano Malam Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar yace komawa makarantun ya shafi makarantun gwamnati da masu zaman kansu.
Sanarwar tace daliban makarantun kwana zasu koma ranar Lahadi 6 ga watan Afirilun shekarar 2025 sannan daliban jeka ka dawo zasu koma ranar litinin 7 ga wata.
Sanarwar ta nemi iyaye da su tabbatar sun kiyaye da wanann sanarwar da aka fitar.
Haka kuma gwamnatin Kano ta bakin kwamishinan Ilimi Gwani Ali Haruna Makoda ya gargadi dalibai da komawa makarantun dauke da abubuwa da aka Hana zuwa dasu da suka hada da Reza da wuka da kayan sanya maye.
Ya nemi Malaman makarantu da su rike aikinsu tsakani da Allah sannan su koma aiki daga ranakun da aka tsara.
Sannan kwamishinan ilimin ya shaida cewa , gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf na iya kokarinsu wajen habaka harkokin ilimi

