Gwamnonin Kudu maso Yammacin Najeriya nuna damuwa tare da bullo da wani shiri na musamman domin tabbatar da tsaro a yankinsu.
A cikin shirin gwamnonin zasu tabbatar dacewa yan bindiga basu cigaba da kai hare hare tare a yankinsu ba.
Rahotanni nacewa Sakamakon yawan simamen da sojojin Najeriya suka matsa kaiwa a maboyar yan ta’adda tare da kashe su a yankin Arewa maso Yamma, yan ta’addar da dama sun fara guduwa suna koma jihohin Kudancin Najeriya.
A ‘yan watannin nan, an samu rahoton yadda aka gano ‘yan bindiga a dazuzzukan Kudu maso Yamma, musamman a jihar Ondo da Ekiti, wadanda ke da iyaka da jihar Kogi.
Har ila yau yankin Arewacin jihar Oyo an samu rahoton yadda yan bindiga suka samu mafaka acan.
A yanzu haka dai gwamnoni guda shida na shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya sunyi taron gaggawa a , Ikeja cikin jihar Lagos domin magance wannan matsalar.
Gwamnonin sun hada da Babajide Sanwo-Olu na Lagos, da Seyi Makinde na Oyo da Dapo Abiodun na Ogun da Ademola Adeleke na Osun da Biodun Oyebanji na Ekiti da kuma gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo.
A wani yanayi na nuna damuwa,gwamnonin yankin sunce ya zama wajibi su tashi tsaye domin hana yan bindigar cigaba da kwarara yankinsu.
Kungiyar gwamnonin ta amince da kafa kungiyar sa ido domin inganta tsaro a fadin yankin Kudu maso Yamma.
Sannan sun tattauna yadda za’a inganta samar da abincin da kulawa da yadda farashin abinci ke hawa da sauka a yankin

