Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya haramtawa malaman makarantu sanya dalibai ayyukan karfi a ciki da wajen makarantun Furamare da sakandire a jihar.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema Labarai.
A cewar sanarwar, gwamnan ya yi wannan gargadin ne a wata ziyarar bazata da ya kai makarantar koyar da harshen Larabci ta SAS da ke birnin Kano, inda ya tarar da dalibai suna tona bututun bayan gida domin gyarawa.
Ya kuma yi alkawarin gyara masallacin Juma’a na makarantar da wasu gine gine dake bukatar gyara.
Sanarwar tace gwamna Yusuf baiji dadin ganin daliban suna gyara wajen bayan gida ba, a dan haka nan take ya dakatar da daliban tare da gargadin cewa kada a sake saka daliban makarantu aikin karfi ko wanne iri ne a cikin makarantu ko wajensu.
Gwamna Yusuf yace daga yanzu babu wani dalibi ko daliba da zasu rikayin aikin karfi a makarantun Kano da sunan horo ko kuma aikin sa kai.
Yace babban makasudin tura dalibai makaranta shine daukar darasi da tarbiya da koyon Sana’a,ba aikin shara ko noma ko wani aikin karfi ba.
Amma da yake maida jawabi a gaban gwamnan na Kano shugaban makarantar ya ce daliban sukanyi irin wannan aiki ne bayan tashi daga makaranta.
Amma nan take gwamnan yace ba zai yiyu ba ,tare da bada umarnin a dakatar.
TST Hausa ta gano cewa ,ba’a sani ba ko umarnin ya shafi daliban makarantun kwana na Kano ,ganin cewa akan saka daliban shara da aikin mako mako na tsaftace makaranta wanda ake kira da LABOR DAY.

