Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), a kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a Katsina.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an sace tsohon Shugaban NYSC din ne da karfe 12:30 na safiyar ranar Alhamis inda wasu mahara dauke da muggan makamai suka abkawa al’ummar garin, inda suka rika harbe-harbe a kai a kai domin sanya fargaba a tsakanin mazauna yankin.
Daga bisani suka tafi dashi.
Har ya zuwa lokacin bayar da rahoton hukumomi ba su bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

