Shugaban Kungiyar Kano one family kuma jigo a jami’yar APCn Kano Alhaji Shehu Isa Direba ya nuna gamsuwarsa kan yadda gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nuna karamcin da mutuntaka a yayin Jana’izar marigayi Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi.
A wani sakon murya da Shehu Isa Direba ya aikewa da TST Hausa yace duk wani dan APC a Kano mutukar yana son zaman lafiya da kishin Kano ta yaji dadin abinda gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nuna na karamcin da dattako a yayin Jana’izar marigayi Galadiman Kano wanda ya rasu ranar Talala data gabata.
Direba yace wannan ya nuna cewa , gwamna Yusuf daga gidan mutunci ya fito kuma shi ne mutum ne da baya dauka da zafi ko kuma a mutu ko ayi rai.
TST Hausa ta rawaito cewa an ta yada hotunan yadda akayi Jana’izar marigayi Galadiman na Kano,wanda yawanci yan siyasa ke cewa ,abinda yan siyasar sukayi abu ne da ya kamata ya zama darasi a garesu musamman na kasa .
“Abu uku ne yafi burgeni da gwamna Abba Kabir Yusuf a yayinda ake Jana’izar marigayi Galadiman Kano,”Inji Shehu Isa Direba.
Na daya yace ,anyi Jana’iza dashi ,na biyu kuma yace yaje har gidan Shugaban APC na Kano Alhaji Abdullahi Abbas yayi masa gaisuwa,na uku Shehu Direba yace gwamna Yusuf ya zauna ana karbar makoki dashi.
Yace duk da zazzafar adawar siyasa dake tsakanin Abdullahi Abbas da gwamna Abba Kabir Yusuf,amma hakan bai hana gwamnan na Kano yin duk abinda ya dace ba.
Shehu Isa Direba yace hakan ya nuna gwamnan jihar Kano dan gidan masu mutunci ne kuma suna fatan hakan zai dore domin cigaba Kano.
Ya kara dacewa abinda gwamnan yayi ,shine fatan Kungiyarsu ta Kano one family,wacce ke fadi tashi dan ganin an daina siyasar tumasanci an sanya kano a gaba.
Yace dole ne su jinjinawa gwamna Yusuf akan abinda yayi.
Ya kuma shaida cewa abinda suke bukata a yanzu shine duk lokacin da aka kammala zabe to a ajiye ra’ayin siyasa a sanya Kano a gaba.
Daga karshe ya mika sakon ta’aziya ga Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas da dukannin yan uwa da abokan arziki da ita kanta gwamnatin Kano akan rashin da akayi na Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi.

