Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Bebeji Hon Aliyu Muhammad Tiga na jam’iyar NNPP ya tallafawa yan mazabarsa da ababan hawa da kayan koyar Sana’a da kudade.
Rahotanni nacewa a kalla mutane 150 ne suka amfana da tallafin.
Tallafin da dan majalisar ya samar ya kai sama da naira Miliyan 60 wanda ya hada da Motoci da , Babura da Injin Ban ruwa, da Kekunan Dinki da kuma tallafin kudi ga mata da maza domin su yi jari su dogara da kansu.
Da yake jawabi a yayin taron bada tallafin, Honarabul Aliyu Muhammad Tiga, ya ce ya basu tallafin ne domin su inganta rayuwar su ta yadda za su dogara da kansu.
A cewar Tiga, “Tallafin dana bayar a yau Laraba ya hadar da Motoci 4, Sabbin babura masu kafa biyu guda 30, Sabbin Kekunan Dinki 30 da kuma Injinan Banruwa ga shugabancin jam’iyyar NNPP na karamar hukumar Bebeji, da na tsohuwar PDP wato Oction A da B na karamar hukumar”.
Suma wadannan suka amfana sun yaba wa dan majalisar, a bisa irin ayyukan alkairin da yake yiwa al’ummar yankin na karamar hukumar Bebeji da kewaye.
Taron ya gudana ne a gidan Dan Majalisar wakilai mai wakiltan kananan hukumomin Kiru da Bebeji, inda ya sami halartar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP da kuma dumbin al’ummar yankin.

