Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi kira ga ‘yan Arewa da ‘yan Nijeriya da su yi hakuri su mara wa Shugaban kasa Bola Tinubu baya a zaben 2027 domin ya karasa Shekarunsa 8.
Da yake jawabi a wajen bikin Nzeh Mada na 2025 a garin Akwanga, gwamna Sule ya ce ko yan Arewa sun marawa Tinubu baya ko basu mara masa baya ba ,zai sake lashe zaben shekarar 2027.
Yace da yawa daga cikin masu cewa Tinubu ba zaiyi tazarce ba a 2027 basu da wani Iko ko karfin fada a Arewa ,a dan haka yace babu abinda zai hanashi tazarce.
Yace kamar yadda shiyar Arewa tayi mulkin Najeriya shekara 8 haka ya zama wajibi shiryar Kudu tayi shekara 8 tana mulki.
Gwamna Sule, wanda shi ne Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya, ya ce wasu ‘yan siyasa daga Arewa na haifar da rudani idan har suka kasa samun abin da suke so ko cimma burinsu na siyasa.
Yace wasu daga cikin tsofaffin gwamnonin sun shaida masa cewa mutumin da ya fi cancantar sake zama shugaban kasa shi ne Bola Ahmed Tinubu a 2027.

