Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar dacewa ba zata biya albashin watan Afirilu ga ma’aikatan Kano ba sai anga kowa Ido na kallon Ido a kokarin gwamnatin na magance zurarewar kuɗaden jama’a aljihun wasu.
Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Umar Faruq Ibrahim ya bayyana hakan a taron manema labarai,kan matakan garambawul da gwamnatin Kano ta dauka na magance yadda ake yankewa ma’aikata albashi da kuma yadda ake biyan wasu albashi alhalin kodai sunyi ritaya ko kuma sun rasu.
TST Hausa ta rawaito cewa a kalla mutane 247 ake biya albashin a duk wata ba bisa ka’ida ba ,da kuɗaden suka wuce sama da naira miliyan 28.
Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Umar yace irin wadannan ma,aikata da ake biyan albashi ba bisa ka’ida ba sun fito ne daga kananan hukumomi da wasu ma’aikatun gwamnati.
“Daga watan Afirilu da yake karewa kowanne ma’aikaci sai ya gabatar da kansa Ido da Ido ya cike takarda kafin a bashi albashin watan Afirilu”Inji Alhaji Faruq.
Yace duk da sun san cewa aikin akwai wahala,amma haka za’ayi hakuri a hada karfi da karfe domin tafiya akan wannan tsari.
Ya shaida cewa daga wannan makon za’a fara biyan albashi amma kowa sai ya gabatar da kansa ,ta hanyar amfani da lambar dan kasa ta NIN da lambar baki ta BVN
Ya nemi ma’aikatan da suyi kyakyawar fahimta ga gwamnatin Kano,yana mai cewa an fito da tsarin ne ba dan muzgunawa ma’aikata ba ,saidai kawai domin kawo gyara.

