Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta fara fuskantar rikicin cikin gida biyo bayan rahotannin da ke cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma Jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa kwankwaso zai bar jam’iyarsa ya koma APCn.
Duk dacewa NNPP ta musanta batun komawar Sanata Kwankwaso APC amma hakan ya janyo tada kura da neman haifar da rabuwar kai a cikin jam’iyar ta APC.
Da yake zantawa da manema labarai a shelikwatar jam’iyyar ta APC a Kano ranar Juma’a, shugaban jam’iyyar APCn na jihar, Abdullahi Abbas yace komawar Kwankwaso jam’iyarsu cigaba ne.
“Muna murna sosai ,kuma Kwankwaso idan ya dawo APC gida ya koma”,Inji Abbas.
Amma a baya bayan nan ,anjiyo shugaban APCn Abdullahi Abbas na gargadin cewa dole ne duk mutanen da a baya suka taba mutuncin Shugaban kasa Bola Tinubu da Mataimakinsa da Shugaban APC na kasa Abdullahi Ganduje da su nemi afuwarsu kafin su koma APCn.
Abdullahi Abbas ya nemi shugabanin jam’iyar APC a matakin jiha da kananan hukumomi da mazabu da su fara aikin yin jirista ga duk wanda yake da sha’awar dawowa APC.
Ya tabbatar dacewa, jam’iyar zata yiwa kowa adalci da wadanda suka koma da Wadanda suke cikinta tun a baya.
Haka kuma ya shaida cewa jam’iyar APC ba zata zamo mafaka ga wadanda suke da laifin cin hanci da rashawa ba.
TST Hausa ta rawaito cewa yayinda Shugaban APC d wasu ya’yan jam’iyar a kano ke maraba da shigowar sanata Rabiu Musa kwankwaso cikin APC duk dacewa NNPP ta musanta hakan ,Amma an samu rabuwar kai tsakanin ya’yan jam’iyar ta APC a Kano.
Rahotanni nacewa wasu na maraba da shigowar Jagoran na kwankwansiyya cikin APC cikinsu harda Abdullahi Abbas mutukar ya nemi afuwar shugabaninta na kasa ,wasu kuwa sun kekasa kasa cewa ba zasu yafewa madugun kwankwansiyyar ba ,koda ya nemi afuwar kuma a shirye suke su fice daga APCn.
Mai magana da yawun APC na jihar Kano, Ahamad Aruwa na daga cikin wadanda sukayi watsi da batun shigowar Kwankwaso cikin APC koda anyi sulhu dashi.
“Ba ma maraba da shi bayan ya tafka kurakurai da dama a kan mutane, yanzu ya nemi ya dawo? Ba za mu yarda da hakan ba, ”in ji Aruwa
Yace a NNPP dinma ya raba kanta gida biyu ,to watakila dabara zaiyi ya kashe APC dan kada tayi nasara a 2027 kamar yadda ya yiwa PDP a kano,Inji Aruwa.

