Katafaren kamfanin sadarwa na MTN ,ya nemi afuwar yan Najeriya saboda Karin kuɗin da yayi akan Data da kiran waya da kaso 200 cikin 100.
Haka kuma MTN ya nemi afuwar yan Najeriya akan matsalolin da aka samu na tangardar hanyoyin sadarwa a kwana biyu.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na X a ranar Alhamis.
Yace karin kuɗin datar da waya kuskure ne ,a dan haka yake neman afuwar yan Najeriya musamman masu saka giga 15.
A sanarwa da MTN ya fitar yace Karin kudin ya sabawa karin kuɗin kiran waya da Data da tura sako da hukumar sadarwa ta kasa NCC ta amincewa Kamfanonin sadarwa da kaso 50 cikin 100.
TST Hausa ta rawaito cewa a wayewar garin yau Alhamis aka tashi da karin, musamman masu amfani da giga 15 zuwa sama inda suka ga kamfanin ya kara kaso 200 cikin 100 maimakon kaso 50 cikin 100.
MTN yace “zuwa gareku masoyanmu masu amfani da giga 15 mun san kun damu to ku yafe mana ,kuskure aka samu.
Sanarwar ta kara dacewa “a cikin wannan lokaci na soyayya, kada ku yi fushi da mu,muna neman gafara kuma ku manta da abinda ya faru.
Saidai rahotanni nacewa neman afuwar da Sanarwar bata shafi Karin kuɗin kiran waya da Data da kaso 50 cikin 100 da MTN yayi ba.
Amma idan za’a iya tunawa a baya bayan nan Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta nemi ‘yan Najeriya da su kauracewa amfani da kamfanonin sadarwa na MTN da AIRTEL da GLO daga ranar 13 ga watan Fabareru har zuwa ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2025 ta hanyar Kashe layukansu daga karfe 11 na safe zuwa karfe 2 na rana.

