Gwamnatin kasar Saudiyya ta bullo da sabbin ka’idojin takaita amfani da takardar shiga kasar ta visa wanda zai shafi matafiya daga kasashe 14 na duniya.
Gwamnatin kasar ta sanar da cewa masu son shiga kasar zasu rika amfani ne da Visa sau daya cikin kwanaki 30 ba tare da wani zabi na tsawaita ta taba.
Saidai kasar ta Saudiyya tace sauye sauyen zai shafi masu yawon bude ido, da matafiya dake zuwa kasuwanci, da waɗanda ke ziyartar dangi, inda kuma tace sauyin bai shafi masu nema zuwa aikin Hajj,da Umrah,ko ma’aikatan Diflomasiyya ba.
Kasashen da sabbin dokokin takaita shiga Saudiyyar suka shafa sun hada da Algeria da Bangladesh da Masar da Habasha da Indiya da Indonesia da Iraqi da Jordan da Morocco da Nijeriya da Pakistan da Sudan da Tunisia da kuma Yemen.
Mahukuntan Saudiyya sunce sun billo da sabbin dokokin takaita shiga kasar ne saboda samun wasu suna amfani da Visa guda biyu ta shiga kasar tare da gano cewa wasu matafiyan suna amfani da Visar ta dogon lokaci don zama a kasar ba bisa ka’ida ba.
Gwamnatin Saudiyya ta kuma tsara yadda za’a gudanar da aikin Hajji ta hanyar kayyade kaso na kowace kasa, sanan mahajjata marasa izini sun taimaka wajen kawo cunkoso acewar kasar.
Kasar tace Lamarin ya yi muni musamman a shekarar 2024, lokacin da mahajjata sama da 1,200 suka rasa rayukansu sakamakon tsananin zafi da cunkoso.
Ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje na shawartar matafiya daga ƙasashen da abin ya shafa da su nemi takardar izinin shiga Saudiyya sau daya kuma su bi sabbin ƙa’idodin domin gujewa hukunci ko kuma kawo cikas ga balaguro

