Fadar shugaban ƙasa ta yi martani kan yada ce-ce-ku-ce yayi yawa tsakanin ‘yan Najeriya game da kashe Naira miliyan dubu 10 dan samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Villa.
Fadar ta shugaban kasa ta fito fili ta kare matakin nata ne bayan ‘yan Najeriya sun matsa lamba ga Bola Tinubu kan ya janye wannan shiri.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya bayyana a shafinsa na X cewa ko a fadar shugaban kasar Amurka ana amfani da lantarki mai amfani da hasken rana.
Onanuga ya fadi haka ne domin nuna cewa amfani da wutar sola a muhimman wuraren gwamnati ba sabon abu ba ne.
Vanguard ta wallafa cewa wutar solar da za a samar a Aso Rock za taba da wuta mai ɗorewa ga gidan shugaban ƙasa,da ofisoshin gudanarwa da kuma wasu muhimman gine-gine.
An bayyana cewa hakan zai ƙara inganta ingancin wutar lantarki da rage dogaro da na’urar janareto, tare da rage kuɗin da gwamnati ke kashewa kan lantarki a tsawon lokaci.
Onanuga ya haɗa da bidiyo na wani aikin samar da sola da aka aiwatar a Fadar White House, inda aka nuna dalilan da suka sa gwamnatin Amurka ta zaɓi amfani da sola a shekarun baya.

