Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa Sarkin Noma na Chiromawa, Alhaji Yusuf Nadabo, ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane da suka yi awon gaba da shi a daren jiya.
Majiyoyin sun ce a halin yanzu Alhaji Yusuf Nadabo yana gidansa da ke Chiromawa, cikin koshin lafiya.
Sai dai, TST Hausa ta rawaito cewa har yanzu ba a samu cikakken bayani kan yadda ya kubuta ba, ko dai jami’an tsaro ne suka kai masa ɗauki, ko kuma ya samu damar kubucewa da kansa daga hannun masu garkuwar.
Lamarin ya faru ne bayan wasu mutane dauke da makamai sun afka wa garin Chiromawa da ke Ƙaramar Hukumar Garun Malam a Jihar Kano, a daren jiya.
Rahotanni sun ce maharan sun bude wuta kan jama’a, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu, kafin daga bisani su yi awon gaba da Sarkin Noman.
A yanzu haka, ana ci gaba da tattara ƙarin bayanai kan harin da kuma yadda Alhaji Yusuf Nadabo ya samu damar komawa gida.

