Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta kalubalanci jam’iyyar NDC da ta yi karin haske kan matsayin aikin Malam jami’a 26 da sunayensu suka bayyana a cikin kwamatin yakin neman zaben gwamnan Kano na NDC.
Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamna na APC a Kano, na biyu Hon. Sanusi Majidadi Kiru,shine ya yi martani inda ya ce jam’iyyar na son NDC ta bayyana ko waɗannan mutane suna da alaƙa da tsarin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar, tare da fayyace ko wasu daga cikinsu ma’aikatan gwamnati ne.
Sunayen mutanen 26 da aka ambata a cikin jerin sun haɗa da:
Prof. Bello Ibrahim
Prof. Abubakar Jafar Usman
Prof. Ahmad Jibril Sulaiman
Prof. Dahiru Sani Shu’aibu
Prof. Taufiq Abubakar Hussain
Ass. Prof. Mansur Hassan
Dr. Ali Kuraish
Dr. Salisu Ahmad Dambazau
Dr. Shuaibu Abdurashid
Dr. Mukhtar Danlami Bunkure
Dr. Muhammad Inuwa Shuaibu
Dr. Umar Danbaito
Dr. Mustapha Shehu Uba Sharada
Dr. Ashiru Sani
Dr. Musa Muhammad Bello Rano
Dr. Muhammad Sulaiman Fagge
Dr. Rabi’u Musa
Dr. Sadiq Uba Jalli
Dr. Nazifi Umar Alaramma
Dr. Abdallah Muhammad Ahmad
Dr. Umar Isa Ahmad Tudun Wada
Dr. Umar Garba Sheka
Dr. Mustapha Yusuf Abubakar
Dr. Tahir Ahmad Ungoggo
Dr. Yusuf Danbaba Dakata
Dr. Abdullahi Garba.
Sanusi Majidadi Kiru ya ce bisa bayanan da suke da su, wasu daga cikin mutanen da aka ambata ma’aikatan jami’o’in gwamnati da sauran hukumomin gwamnati ne a Kano, waɗanda ke karɓar albashi da sauran alawus-alawus a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya bayyana cewa duk da wannan, APC ba ta taɓa amfani da matsayinsu na aiki wajen tsoratar da su ko hana su bayyana ra’ayinsu na siyasa ba, saboda jam’iyyar ta yi imanin cewa kowane ɗan ƙasa na da ’yancin zaɓar ƙungiyar siyasar da yake so.
Wannan martani na APC na zuwa ne bayan wata sanarwa da aka danganta ga ɗan takarar gwamnan NDC a Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, inda ya yi gargaɗin cewa ma’aikatan gwamnati waɗanda sunayensu suka bayyana cikin jerin masu goyon bayan APC za su fuskanci sakamako mara kyau idan jam’iyyarsa ta karɓi mulki.
Sanusi Kiru ya ce wannan gargaɗi ya haifar da tambayoyi kan ko ma’aikatan gwamnati za su fuskanci korar aiki, sauya musu wurin aiki zuwa wurare masu nisa, hana su samun ƙarin girma ko kuma ƙirƙiro zarge-zargen ladabtarwa domin hukunta su saboda bambancin ra’ayin siyasa.
Ya jaddada cewa aikin gwamnati mallakin jiha da al’ummarta ne, ba na kowace jam’iyyar siyasa ba, don haka bai kamata a mayar da haƙƙin ma’aikata da ci gaban aikinsu abin dogaro da jam’iyyar da suke goyon baya ba.
A cikin sanarwar, APC ta kuma yi nuni da sashe na 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, wanda ya tanadi ’yancin haɗa kai da shiga ƙungiyoyi, ciki har da ƙungiyoyin siyasa.
Sai dai jam’iyyar ta amince cewa akwai dokokin aikin gwamnati da ke tsara wasu nau’o’in shiga harkokin siyasa ga ma’aikata, tana mai cewa ya kamata a bambanta haƙƙin ɗan ƙasa na zaɓar jam’iyya da kuma wajibcin bin ƙa’idojin aikin gwamnati.
Sanusi Kiru ya kuma yi amfani da karin maganar nan cewa, “Duk wanda ya zo neman adalci, dole ne shi ma ya kasance mai gaskiya”, inda ya buƙaci NDC ta yi wa kanta irin binciken da take son yi wa wasu.
A ƙarshe, APC ta yi kira ga Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo da shugabancin NDC su fito fili su fayyace matsayinsu, tare da tabbatar wa al’ummar Kano cewa babu wani ma’aikacin gwamnati da zai fuskanci korar aiki, sauya wurin aiki, hana ƙarin girma ko tsangwama saboda goyon bayan wata jam’iyyar siyasa.
Jam’iyyar ta ce ya kamata a gudanar da fafatawar siyasa bisa adalci, bin doka da mutunta haƙƙin kowane ɗan ƙasa, ba tare da amfani da barazana ko tsoratarwa ba.

