Wata kotun shari’ar Musulunci da ke unguwar Sharaɗa, a cikin harabar hedikwatar Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta yanke wa wata matashiya mai suna Zainab Abubakar, mai shekaru 19, hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni biyar tare da bulala 10, ba tare da zaɓin biyan tara ba.
An yanke mata hukuncin ne bayan ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi, wanda ya shafi kalaman zagi da ta wallafa a dandalin sada zumunta na TikTok, waɗanda suka shafi Hukumar Hisbah da Babban Kwamandanta, Malam Aminu Ibrahim Daurawa.
A zaman shari’ar da Mai Shari’a Bashir Abdullahi Ibrahim ya jagoranta, an kuma gurfanar da wasu matasa biyu, Ahmad Usman, wanda aka fi sani da Ortega, mai shekaru 25, da Muhammad Aliyu, mai shekaru 20.
Ana zargin Zainab da aikata laifin zagi wanda ya saɓa wa tanadin sashe na 312 na dokar Penal Code.
Sai dai Ahmad Usman da Muhammad Aliyu sun ƙaryata zargin haɗa baki wajen cin mutuncin Hukumar Hisbah da kwamandanta.
Bayan lauyansu ya gabatar da buƙatar neman belinsu, kotun ta bayar da umarnin ci gaba da tsare su a gidan yari na tsawon makonni biyu, domin samun damar duba batun belin nasu.
Haka kuma, kotun ta umarci ɓangaren masu gabatar da ƙara da su tabbatar sun shirya shaidu domin ci gaba da shari’ar.

