Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya shaida hakan ne a wata hira da BBC Hausa domin karin bayani kan Abubuwan da suka faru tsakaninsa da Zainab Kwankwaso.
Yace abubuwan da suka faru tun da jimawa abin takaici ne musamman yadda aka kwashe masa kayan dakin matarsa aka kuma tafi da ita a karshe aka kaishi Kotu a Abuja.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce batun yana gaban kotu a yanzu kuma bai kamata a saka siyasa a batun aurensa ba tun a baya.
Ya ci gaba da cewa: “Ita dai wannan mata, Zainab ƴar wansa ce (Kwankwaso), kuma ya yi masu aure amma ita auren nata bai daɗe ba, daga nan Allah Ya haɗa mu muka yi aure kimanin shekara 20 da suka wuce, kuma muna da yara.
Ya ce duk da cewa ba zai faɗa wa duniya yadda aka bi wajen ɗauke matar tasa daga gidansa ba, amma yana da shaidu da bayanai dalla-dalla kan yadda lamarin ya faru.
A cewarsa wannan bai kamata ya zama abin cece-ku-ce kasancewa abu ne da aka saba ganin irin hakan.

