Wani magidanci Alhaji Musa Ibrahim Daura da yayi ikirarin cewa shi dan uwa ne ga marigayi tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin gabatar da kansa ga iyalan Buhari a Daura ranar Asabar mai zuwa.
Alhaji Musa Daura dan asalin kauyen Kosarawa a Daura dake Jihar katsina,yace sun hada jini ne da marigayin ta bangaren kakarsa ta wajen Uwa da ita Kuma ta kasance yar uwa ce ga mahaifin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rasu ranar Lahadi.
TST Hausa ta rawaito cewa a wata hira da Rahma Radiyo da Talabajin a birnin Kano , magidancin yace tun wa’adin mulkin tsohon shugaban na biyu yake ta fadi tashin ganin dan uwansa amma hakansa bai cimma ruwa ba.
“Jami’an tsaro ne suke hanani shiga fadar shugaban kasa ,sannan suke dakile ni daga ganin dan uwana”Inji Musa Daura.
Da aka tambayeshi ko marigayi Buhari din ya sanshi, sai yace eh,domin kuwa ya taba tambaya ta da yaje hutu Daura cewa Ina wanda akaje dani Riga sunansa tun Ina karami ,akace baya nan.
Tabbas, Buhari yaje bikin suna na yana da shekaru 13 , Wannan maganar kakata ce take fadan kafin ta rasu.”Inji Musa Daura.
Ya kara dacewa ,duk wanda ya ganni musamman dangi ga tsohon shugaban Kasar Buhari zai yarda cewa mun hada jini ,daga kamannin da muke da juna ma ,ya Isa shaida.
Rahotanni nacewa tun a shekarar 2022 kafin Buhari ya bar mulkin Najeriya,yace Bashir Ahamad ya nemi ganawa dashi,bayan ya saurari bukatarsa a Rahma Radio,amma bukatarsa bata biya ba
Zuwa yanzu Musa Ibrahim Daura yaci alwashin tafiya garin Daura a jihar Katsina, domin gabatar da kansa wajen iyalan marigayi Buhari ko zasu gane shi.
Yace rabon Buhari da kauyensu na Kosarawa,tun shekarar 1984 lokacin Buhari yana mulkin soja.
Bukata ta iyalansa su gane ni,saboda shi bashi da ragowar yan uwa da yawa.