Jigo a jam’iyyar NNPP kuma dattijon kasa, Alhaji Buba Galadima, ya bayyana alhininsa tare da girgiza bisa rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda suka taba yin aiki tare a baya.
A wata hira da aka yi da shi a DW International Radio a daren Litinin, Galadima ya ce bai taba tunanin mutuwar Buhari nan kusa ba, kuma ya ce kamar yadda addinin Musulunci ya koyar, mutuwa hanya ce da kowa zai bi ta.
Galadima ya kara da cewa ya riga ya yafe wa Buhari duk wani abin da ya taba masa rai, ko da an yi shi da gangan ko ba da gangan ba, kamar yadda uwargidan marigayin, Aisha Buhari, ta nemi afuwa ga mijinta a madadinsa kafin rasuwarsa.
Galadima ya bayyana Buhari a matsayin dan kasa na gaskiya wanda yake da cikakken imani da kishin Najeriya.
Ya ce duk da yadda abubuwa suka kasance a lokacin shugabancinsa, Buhari amma ya yi kokari matuka.
Galadima ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, ‘yan uwansa da kuma daukacin al’ummar Najeriya, yana mai bayyana rasuwar Buhari a matsayin babban rashi ga kasa.
Ya kuma ce yana karbar sakonnin ta’aziyya daga mutane da dama a cikin gida da wajen Najeriya, wadanda suka san cewa sun taba yin aiki tare da Buhari na tsawon lokaci.

