Yayinda aka kammala jana’izar Attajirin dan kasuwa Alhaji Aminu Alassan Dantata a birnin Madina,an hango hotuna daban daban da aka dauka tsakanin yan siyasar Kano, musamman wadanda ake ganin basa ga maciji.
A nazarin da gogaggen dan Jarida Adamu Dabo yayi,kuma TST Hausa ta wallafa,ya nuna cewa da alama jana’izar Attajirin Dantata ta sada zumunci tsakanin yan siyasar na Kano.
Misalin hakan shine yadda a masallacin Annabi Muhammad SAW aka gango tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Shugaban jam’iyar APC na ƙasa Dr Abdullahi Umar Ganduje tare da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa suna gaisawa .
A watan da ya gabata ne tsohon gwamnan jihar ta Kano ake zargin cewa ya baiwa yan sanda umarnin kama Hon Sunusi Bature Dawakin ruwa a jallo saboda zargin bata suna,saidai har yanzu Sunusi Bature din bai kamu ba.
An jima ana tsamin dangantaka tsakanin Hon Sunusi Bature Dawakin Tofa da Dr Ganduje akan abinda ya shafi siyasar Dawakin Tofa da ta Kano baki daya.
Sunusi Bature yasha kalubalantar Siyasar Ganduje musamman rashin tabuka abin azo a gani da kuma zarge zarge na cin hanci da rashawa.
Saidai Dr Ganduje da magoya bayansa sun sha musanta hakan.
TST Hausa ta rawaito cewa a yanzu haka abinda Hon Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya a gaba shine zamowa dan majalisar tarayyar mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Tofa da Tofa da Rimin Gado a shekarar 2027.
