Daya daga cikin jagorori a jam’iyar APC mai mulkin kasa Hon. Shehu Isa Direba ya nesanta tsohon Shugaban jam’iyar APCn ta kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga kalamai marasa kan gado da yace wasu yan Adawa na jifan Ganduje dasu bayan saukarsa daga Shugabancin APC ranar Juma’a.
Shehu Isa Direba wanda tsohon mai baiwa Dr Ganduje shawara akan harkokin yada Labarai ne lokacin yana mulkin Kano,ya shaida cewa tsohon Shugaban APCn Dr Ganduje ba zai tabe a siyasar Najeriya ba.
Ya kuma musanta cewa ,saboda kokarin shigowar tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa kwankwaso cikin jam’iyar ta APC ne yasa Dr Ganduje ya ajiye mukaminsa.
“Shigar Kwankwaso APC idan ma da gaske ne bashida alaka da ajiye mukamin da Ganduje yayi ranar Juma’a”;Inji Direba.
Yace Dr Ganduje ya sauka ne domin kare martabar musulunci a siyasance .
Ya roki yan adawa da su daina yada jita jitar da basu da masaniya akanta ,saboda siyasa.

