Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe sama da naira miliyan dubu 3 domin biyawa daliban jihar Kano Jarabawa neman shiga makarantun gaba da sakandire ta NECO.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano Alhaji Ali Haruna Makoda ne ya tabbatar da hakan a yayin ganawarsa da manema labarai a ofishinsa a ranar Juma’a.
Kwamishinan yace Dalibai 141,715 ne suka rubuta Jarabawar neman cancantar samun damar rubuta NECO kyauta daga gwamnati ko kuma dalibi ya biya da kansa da akafi sani da jarabawar Qualifying,Inda ya shaida cewa kaso 75 cikin 100 na daliban sun samu nasara.
TST Hausa ta rawaito daliban da suka samu nasara da cancanta na biya musu daga gwamnatin,sun samu credit biyar ne kowannensu.
Daliban da zasu amfana da kuɗin tallafin sun hada da wadanda zasu rubuta jarabawar NECO da NAPTIB da NBAIS.
“Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika Gwarzo,kuma yace yana taya daliban Kano murna,”Inji kwamishinan na ilimi Makoda.
Ali Makoda yace biyawa daliban jihar Kano jarabawar ta NECO,yana daga cikin burin gwamnati na ingata ilimi a Kano.

