Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana Talata, 15 ga watan Yuli, 2025, a matsayin ranar hutu na musamman domin jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi a birnin London na ƙasar Birtaniya.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta fitar a yau Litinin, wadda Babbar Sakataren Ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya fitar da sanarwar a madadin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa wannan hutu wata alama ce ta ƙarin girmamawa da karramawa ga rayuwa da hidimar marigayin shugaban ƙasa.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ayyana ranar Talata a matsayin hutu domin bai wa ’yan ƙasa damar tunawa da irin gudummawar da marigayin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayar ga ci gaban ƙasa,” in ji Tunji-Ojo
Ya ce marigayin Buhari ya shugabanci Najeriya da jajircewa, gaskiya, amana da sadaukar da kansa, musamman wajen ganin an samu haɗin kan ƙasa da zaman lafiya
Ministan ya ƙara da cewa: “Wannan hutu wata dama ce ta musammam ga ’yan Najeriya domin tunawa da irin rawar da Buhari ya taka wajen jagorantar ƙasa da kuma ƙoƙarinsa na tabbatar da daidaito da ci gaba a tsakanin yankuna.
Suma Kungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun bada hutu a gobe talata.

