Shugaban jam’iyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ajiye aiki a matsayin shugaban APC na kasa.
Ajiye aikin nasa na zuwa ne bayan ya dauki tsawon lokaci a matsayin shugaban APC din.
Wata majiyar sirri ta tabbatar dacewa, Ganduje ya ajiye aiki ne saboda rashin lafiya,Inda zaije ya kula da lafiyarsa.
TST Hausa ta rawaito cewa wasu na ganin ajiye aikin masa na da nasaba da irin kalubalen da APC din ke fuskanta a Najeriya karkashin jagorancinsa.
Abu na baya bayan nan shine yadda aka tada kura a yankin Arewa maso gabas lokacin taron APC na shiryar Inda aka rika jawabai akan takarar Tinubu ta 2027 ba tare da kama sunan mataimakinsa Kashim Shettima ba.
Wata majiya ta shaida cewa ,a kwanan nan wasu jiga jigan APC din sun gindaya sharadin cewa ba zasu goyi bayan Tinubu ba ,a 2027 har sai Ganduje ya sauka daga Shugabancin APC .
