Gwamnatin Jihar Kano ta amince da Sauye-Sauyen wuraren aiki ga wasu ma’aikata da yan siyasa zuwa hukumomin gwamnati.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar yace gwamna Yusuf ya dauki matakin ne domin inganta ayyuka da karfafa shugabanci a hukumomin gwamnati.
Sanarwar ta lissafo wadanda sauyen – sauyen ya shafa.
1. Dr. Muhammad S. Khalil, wanda kafin yanzu shi ne Sakatare na Hukumar Kula da Bin Doka kan tsaftace muhalli wato WECCMA a yanzu ya koma mai rikon mukamin Shugaban hukumar kwashe shara ta Kano wato REMASAB.
A ranar 13 ga watan Fabareru na shekarar 2025 ne , tsohon Shugaban hukumar ta REMASAB Ahamadu Haruna Zagon ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
2. Lamin Mukhtar Hassan, wanda ya kasance Mataimakin Manajan Darakta na REMASAB, yanzu an tura shi zuwa mataimakin Shugaban hukumar tabbatar da ingancin ayyukan gwamnati.
3. Mustapha Sulaiman Mainasara, wanda ke matsayin Babban mai dauko rahoto a hukumar REMASAB,a yanzu an tura shi zuwa hukumar kula da ayyukan noma tsirrai da kiwon dabbobi ta Kano domin ci gaba da aiki a wannan matsayi.
4. Dr. Mahmoud Abba an nada shi a matsayin Mukaddashin Sakatare na Hukumar Kula da Bin Doka kan Sharar Gida (WECCMA).
Gwamnatin Jihar Kano na fatan sabbin jami’an da aka tura za su yi amfani da kwarewarsu da kwazon su wajen sauke nauyin da aka dora musu bisa yadda ya dace.

