Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce a cikin shekaru biyu masu zuwa, Kamfanonin sa za su rika samun ribar kudin shiga na Dala Miliyan 7 a kullum.
Wannan adadi ya yi daidai da Naira miliyan dubu 11 a kowace rana da kamfanin zai rika samu daga fitar da takin zamani zuwa kasashen waje.
Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na zuwa ne a lokacin da Hukumar kula da tashoshin Jiragen ruwa ta Najeriya (NPA) ke hada gwiwa da Kamfanin Dangote domin fadada harkokin fitar da kaya daga Najeriya zuwa kasashen waje.
Hukumar NPA ta ce tun lokacin da aka fara tsarin sayar da danyen mai a Naira a watan Oktoban 2024, jiragen ruwa guda 57 mallakar Kamfanin Dangote take kula da su duk wata.
A yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar hukumar NPA a Legas, Dangote ya fadi muhimmancin inganta mu’amala tsakanin bangarorin biyu.
Alhaji Aliko Dangote ya ce girman ayyukan kamfaninsa da ke Lekki kadai zai hada da jigilar gangar danyen mai har zuwa jiragen ruwa 240.
Ya ce kowanne jirgi na dauke da gangar mai miliyan daya, kuma za a fitar da samfuran man da za su kai kusan jiragen ruwa 600 a shekara.

