Rahotanni daga wajen taron jami’yar APC daga Arewa maso gabas na cewa an samu saɓani a taron shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a Jihar Gombe.
Rikicin ya fara ne bayan da Kwamared Mustapha Salihu, Mataimakin Shugaban APC na ƙasa mai kula da Arewa Maso Gabas, ya bayyana goyon bayansa ga takarar Shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takara a karo na biyu.
Sai dai bai ambaci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ba.
Manyan jiga-jigan jam’iyyar APC daga yankin sun halarci taron, ciki har da gwamnoni,da ministoci, da ‘yan majalisa.
TST Hausa ta rawaito daga wasu kafafen yada labarai cewa Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci taron.
Bayan Salihu ya gama jawabi, wasu daga cikin mahalarta taron sun fusata.
Take suka fara yi masa ihu, wasu ma suna barazanar kai masa hari.
Sai jami’an tsaro suka fito da shi daga ɗakin taron domin kare lafiyarsa.
Don kwantar da rikicin da ya taso, Mataimakin Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Bukar Dalori, ya fito ya bayyana goyon baya ga Tinubu da kuma Shettima don su ci gaba da mulki.
Amma lamarin ya ƙara dagulewa bayan da Ganduje ya yi jawabi, inda ya ayyana goyon bayansa ga Tinubu kaɗai, ba tare da ya ambaci Shettima ba.
A lokacin da yake jawabi Ganduje wanda ya yi kusan minti 10,yana jawabi bai ambaci sunan Shettima ba.
Shi ma sai da jami’an tsaro suka fita da shi daga wajen taron saboda gudun rikicin da zai je ya dawo.
Shettima dai ɗan Jihar Borno ne, ɗaya daga cikin jihohin yankin Arewa Maso Gabas.
Mutane da dama sun ji ba ɗadi kan rashin ambaton sunan a wajen taro da aka yi a yankinsa.
Taron ya kare cikin gaggawa saboda tashin hankali.

