Hukumar kula da zurga zurgar ababen hawa da kiyaye dokokin hanya ta jihar Kano KAROTA ta kama direban wata motar gida saboda zarginsa da karya dokar tuki.
Hukumar ta karota ta kama direban ne akan titin Murtala Muhammad dake birnin Kano bayan ya tsallaka titi ta wajen da bai dace ba ,tare da taka fulawar titi da gwamnatin Kano ta kawata titin da su.
A wata ganawarsa da manema labarai maimagana da yawun hukumar ta KAROTA Malam Abubakar Ibrahim Sharada yace direban ya karya dokar hanya kuma za’a gabatar dashi a gaban kotu domin zama izinina ga masu kokarin karya dokar tuki a kan hanya.
Yaja kunne direbobi da su guji karya dokar hanya,yana mai cewa hukumar ta KAROTA ba zata zura idanu ba.
An zargin Direban da yiwa yan karota din gadara.
Tunda farko mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin yada Labarai Hon Ibrahim Adam shine ya wallafa yadda diraban ya karya dokar tuki,kuma hakan yaja hankalin hukumomin da abin ya shafa aka kamo diraban.
TST Hausa ta rawaito cewa,a watan da ya gabata ne gwamnatin Kano ta gurfanar da wasu masu awakai a gaban kotu saboda ya bar awakansa sunci fulawar tsakkiyar titunan birnin Kano.