Limamin masallacin juma’a na Usman Bn Affan dake Kofar Gadon Kaya a karamar hukumar Gwale Dr. Abdullah Gadon Kaya, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su rungumi haƙuri a kowane fanni na rayuwa, yana mai bayyana cewa rayuwar duniya cike take da jarabawa, kuma babu wata hanyar tsallake su face yin haƙuri da dogaro ga Allah.
Malamin ya bayyana hakan ne a cikin wata huduba mai taken “Haƙuri da Rayuwar Duniya”, inda ya yi bayani dalla-dalla kan yadda Musulmi zai kasance mai juriya yayin fuskantar ƙalubale daban-daban na rayuwa.
A cewarsa, al’umma na fuskantar matsaloli da dama kamar rashin tsaro da tsadar rayuwa da talauci da rashin lafiya da sauran jarabawa, amma abin da Allah Ya fi so daga bayinsa shi ne su kasance masu haƙuri tare da ci gaba da neman mafita ta halal da kuma yawaita addu’a.
Dr. Abdullah Gadon Kaya ya kuma yi tsokaci kan muhimmancin haƙuri da iyaye, yana mai gargadin cewa duk wanda ya raina ko ya ƙi biyayya gare su, zai gamu da sakamakon hakan tun a duniya.
Ya ce:
“Duk wanda ya ƙi biyayya ko ya tozarta iyayensa, wallahi sai ya tozarta shi.”
Malamin ya bayyana cewa girmama iyaye na daga cikin manyan umarnin Allah da ManzonSa (SAW), yana mai cewa duk wanda ya kyautata musu zai samu albarka da ɗaukaka, yayin da raina su kan jawo ƙasƙanci da rashin nasara a rayuwa.
Haka kuma, ya yi kira ga al’umma su yi haƙuri ko da suna rayuwa ƙarƙashin shugabanni marasa adalci, yana mai cewa Musulmi ya kamata ya guji tada fitina, ya riƙa yi wa shugabanni addu’ar Allah Ya shirye su, tare da bin hanyoyin gyara da addini ya tanada.
A wani ɓangare na hudubar, Dr. Abdullah Gadon Kaya ya yi amfani da ibadar Hajji a matsayin babban misali na muhimmancin haƙuri.
Ya ce duk wanda ya je aikin Hajji zai fahimci cewa ibadar gaba ɗaya tana buƙatar juriya, inda ya ambaci layukan banɗaki, cunkoso a Mina, zaman Arfa, kwana a Muzdalifa, jifan Jamarāt da sauran wahalhalu da mahajjata ke fuskanta kafin su kammala ibadarsu.
A cewarsa, waɗannan wahalhalu darussa ne da Allah Ya tanadar domin koyar da bayinsa haƙuri, juriya da biyayya.
Malamin ya kammala hudubarsa da kira ga al’umma da su rungumi haƙuri a cikin dukkan al’amuransu, su girmama iyaye, su yi juriya a lokacin ƙunci da wadatar rayuwa, tare da yawaita istigfari da addu’a.
Ya ce duk wanda ya yi haƙuri saboda neman yardar Allah, Allah zai sauƙaƙa masa al’amuransa, Ya ɗaukaka darajarsa, kuma Ya ba shi kyakkyawan sakamako a duniya da lahira.

