Masana harkokin lafiya da noma sun sake jaddada gargadi kan al’adar shanya amfanin gona a gefen manyan hanyoyi a Najeriya, suna bayyana cewa dabi’ar na jefa lafiyar al’umma cikin hatsari tare da tauye ingancin abincin da jama’a ke ci a kullum.
A yawancin yankunan ƙasar nan musamman karkara da gefen manyan tituna, manoma kan shanya amfanin gona da suka hada da rogo da masara da shinkafa da wake da barkono da tumatir da albasa da Agushi a bakin hanya domin su bushe bayan girbe su daga gona.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/agwamnatin-tinubu-ta-janye-kiranta-ga-yan-najeriya-na-su-fara-azumin-kwana-uku-saboda-karancin-abinci-a-kasa/
TST Hausa ta rawaito cewa amfani da wannan hanya ta zama ruwan dare sakamakon talauci,da rashin kayan busarwa na zamani da kuma raunin kayan aikin bayan girbi.
Sai dai masana sun bayyana cewa, yayin da motocin da sauran ababan hawa ke wucewa a kan hanyoyi, kura mai ɗauke da hayakin mota,da datti da ƙananan sinadarai masu cutarwa na sauka kai tsaye kan wadannan amfanin gona.
Sun ce hakan na iya janyo gurɓatewar kayan abincin sannan ƙwayoyin cuta ka iya shiga musamman kananan ƙarafa da ido baya iya gani da wasu sinadarai da ke iya illata lafiyar dan Adam.
A cewar masana, ci gaba da cin irin wannan abinci na dogon lokaci na iya haddasa matsalolin lafiya musamman ga yara,da mata masu juna biyu da tsofaffi, ko da kuwa ba a ganin illa nan take.
Sun kuma nuna cewa wannan dabi’a na iya ƙara yawaitar cututtuka da ba a gano musabbabinsu da wuri.
A wurare da dama da ake shanya amfanin gona, a kan hango awakai da kaji suna yawo suna taka su.
Wannan yanayi ya ƙara nuna irin barazanar tsafta da ke tattare da al’adar busar da kayan gona a bakin hanya.
Wata masaniyar abinci mai gina jiki, Mrs. Helen Okorie, ta bayyana matuƙar damuwa kan lamarin, inda ta ce duk lokacin da dabbobi suka taka ko suka yi mu’amala da abinci, suna shigar da ƙwayoyin cuta, tsutsotsi da kuma najasa, abin da ke mayar da abincin haɗari ga lafiyar dan Adam.
Ta bayyana cewa cin irin wannan abinci na iya haddasa cututtuka iri-iri, musamman ga yara, mata masu juna biyu da tsofaffi, tare da kira ga manoma da ’yan kasuwa da su ɗauki hanyoyin busarwa masu tsafta domin kare lafiyar jama’a.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/farashin-kayan-abinci-ya-sauka-sosai-amma-takin-zamani-da-zamuyi-amfani-da-shi-yanzu-yafi-karfinmu-manoma/
Baya ga barazanar lafiya, masana sun ce shanya amfanin gona a bakin hanya na rage daraja,da tsafta da ingancin kayan gona, lamarin da ke hana su cika ƙa’idojin tsaron abinci da ake bukata a manyan kasuwanni da ma kasashen waje.
Wannan na kawo cikas ga bunƙasar kasuwancin noma da ƙoƙarin fitar da kayan gona zuwa waje.
Masana sun shawarci manoma da ’yan kasuwa da su daina amfani da bakin hanya wajen busar da amfanin gona, su koma hanyoyi masu aminci kamar rumfunan busarwa, tabarmomi da aka ɗaga daga ƙasa, ko injinan busarwa na zamani. Sun kuma yi kira ga gwamnati a matakai daban-daban, tare da ƙungiyoyi masu zaman kansu, da su zuba jari a fannin kayan aikin bayan girbi, domin kare lafiyar jama’a, rage asarar amfanin gona da inganta harkar noma a Najeriya.

