Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu wa’adin kwanaki bakwai da ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin kafa wata hukumar gwamnati, yana mai gargadin cewa yin shiru kan lamarin na iya sa gwamnati ta zama mai hannu ko kuma mai kare waɗanda ake zargi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya bayyana cewa zargin da ke tattare da kafa sabuwar hukumar ta bogi, ya tayar da hankalin jama’a, saboda haka wajibi ne gwamnatin tarayya ta fito fili ta gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci domin gano hakikanin abin da ya faru.
Ya ce idan har ba a fara bincike cikin kwanaki bakwai ba, hakan zai ƙara jefa shakku a zukatan ‘yan Najeriya tare da haifar da tambayoyi kan aniyar gwamnati wajen yaƙi da cin hanci, da rashin gaskiya da amfani da sunan gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.
Atiku ya jaddada cewa kare mutuncin hukumomin gwamnati da tabbatar da bin doka shi ne ginshiƙin dimokuraɗiyya, yana mai cewa babu wanda ya kamata ya kasance a sama da doka, komai matsayinsa.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da na yaƙi da cin hanci da rashawa su gudanar da bincike mai zaman kansa, tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a gaban kotu idan bincike ya tabbatar da aikata wani laifi.
A cewarsa, yin cikakken bincike da hukunta masu laifi zai taimaka wajen dawo da amincewar jama’a ga gwamnati da kuma tabbatar da gaskiya, riƙon amana da bin doka a harkokin mulkin ƙasa.

