Kungiyar Patriotic Volunteers dake fafutuka kan samar da shugabanci na gari ta karrama wasu ’yan jarida shida a Jihar Kano, bisa la’akari da gudunmawar da suke bayarwa wajen wayar da kan jama’a da kuma inganta shugabanci na gari.
Kungiyar ta bayyana cewa ’yan jaridar sun taka muhimmiyar rawa wajen isar da bayanai ga al’umma, bayyana matsalolin da suke fuskanta da kuma wayar da kan jama’a kan harkokin mulki da shugabanci.
Wadanda aka karrama sun hada da Bello Habib Galadanchi (Dan Bello), Dambello, Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano, Salamatu Sabo B/Zuwo, Abbas Salisu Sorondinki da Jafar Jafar.
A yayin bikin karramawar, kungiyar ta ce aikin jarida na da muhimmiyar rawa wajen karfafa shugabanci na gari, domin ’yan jarida na taimakawa wajen tabbatar da cewa bayanai sun isa ga jama’a, tare da bai wa al’umma damar bayyana ra’ayoyinsu da damuwarsu.
Ta kuma jaddada bukatar ’yan jarida su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin kwarewa, gaskiya da rikon amana, musamman wajen yada bayanan da suka shafi al’amuran jama’a.
Kungiyar ta ce irin wannan karramawa na daga cikin hanyoyin nuna godiya ga wadanda take ganin suna bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’umma da karfafa tsarin shugabanci na gari.
An bukaci sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafa wa aikin jarida da sauran hanyoyin wayar da kan jama’a domin samun al’umma mai cikakken bayani da fahimtar hakkokinta.

