Wani likitan lafiya kuma malami a Jami’ar Bayero da ke Kano, Dr. Najib Bello, ya yi gargadi kan illolin da ka iya tattare da yawan cin naman Kaza, yana mai cewa hakan ba wata alama ce ta jin daɗin rayuwa ba, musamman idan aka yi watsi da daidaito wajen cin abinci.
TST Hausa ta rawaito cewa likitan ya yi wannan gargadin ne a cikin wani shiri na fadakarwa kan nau’o’in abinci da ya kamata mutane su rika ci da kuma wadanda ya kamata su kula da yawan amfani da su.
Yace yawan cin namam kaza na haifar da illoli ga maza musamman karancin kuzari ga iyalansu.
Dr. Najib Bello, wanda malami ne a Sashen Harhada Magunguna na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya jaddada cewa kula da lafiyar jiki na bukatar kulawa ta musamman wajen zabar abincin da ake ci.
Ya kuma bayyana muhimmancin cin abinci iri-iri masu gina jiki, tare da kiyaye daidaito wajen cin abinci, domin guje wa matsalolin lafiya da ka iya tasowa sakamakon rashin ingantaccen tsarin abinci.
A cewarsa, ya kamata mutane su fahimci cewa samun ingantacciyar lafiya ba ya rataya ne kawai kan yawan abincin da mutum ke ci, sai dai irin abincin da yake ci da kuma yadda yake kula da lafiyarsa.
Ya bukaci mutane su mayar da hankali wajen cin ganye da kayan itatuwa.

