Shugaban hukumar bunkasa fasahar halittu da Bincike ta Kasa (NABDA), Farfesa Abdullahi Mustapha, ya bayyana cewa kayan gona da aka samar ta hanyar fasahar GMO wato genetically modified organism ba shi da wata illa ga lafiyar al’umma,ko kasar noma , illa ma suna da matuƙar amfani wajen magance matsalar abinci a Najeriya.
Farfesa Mustapha ya yi wannan bayani ne yayin da yake karin haske kan damuwar da wasu ke nunawa game da amfani da irin wadannan kayayyaki na GMO.
Ya ce yawanci irin wannan tsoro yana fitowa ne daga rashin isasshen bayani da kuma tsoron abin da ba a fahimta ba.
Ya bayyana cewa babu wani samfurin GMO da zai shiga kasuwannin Najeriya sai an yi masa cikakken bincike, sannan Hukumar Kula da Fasahar Halittu ta Kasa (NBMA) ta tabbatar da amincinsa.
Shugaban NABDA ya ce hukumar na ci gaba da wayar da kan jama’a musamman matasa da manoma ta hanyar shirye-shiryen horo da fadakarwa domin su fahimci amfanin fasahar halittu.
A cewarsa, amfani da GMO na taimakawa wajen samar da karin amfanin gona, rage yaduwar kwari da cututtuka, da kuma kara juriya ga sauyin yanayi.
Ya kuma jaddada cewa fasahar GMO ba za ta maye gurbin noma na gargajiya ba, sai dai za ta kara karfafa shi, domin inganta rayuwar manoma da kuma tabbatar da wadatar abinci a kasar.
TST Hausa ta rawaito cewa a baya bayan nan yan Najeriya da dama na nuna fargabar amfani da fasahar ta GMO a aikin noma kasancewar ana zargin muddin akayi amfani da shi ba za’a kara amfani da Kasar noma ta wajen ba sai bayan shekara 25 sannan ga illa ga lafiyar jama’a.
Saidai hukumar binciken tace wanann tunani jita jita ne kuma bashida rushe balle makama

