Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da kuma hukumomin tsaro bisa yadda suka tabbatar da gudanar da zaɓen cike gurbi cikin kwanciyar hankali da tsari a Jihar Kano.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.
Gwamnan ya bayyana zaɓen a matsayin wani muhimmin mataki a tafiyar dimokuraɗiyyar jihar, yana mai cewa yanayin zaman lafiya da aka samu a rumfunan zaɓe ya nuna yadda al’ummar Kano ke ƙara fahimtar muhimmancin siyasa mai tsafta, tare da tasirin ingantattun shirye-shiryen tsaro da aka shimfiɗa.
Ya kuma yaba wa al’ummar mazabun kananan hukumomin birnin Kano da Ungogo a Majalisar Dokokin Jihar, inda aka gudanar da zaɓen, bisa haɗin kai, da ladabi da jajircewa wajen shiga aikin zaɓe cikin lumana.
Gwamna Yusuf ya jinjinawa jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki, musamman ya yan Jami’yar APC bisa bin dokoki da ƙa’idojin zaɓe tare da kauce wa duk wani abu da ka iya tayar da zaune tsaye.
A cewarsa:
“A karon farko cikin tarihin baya-bayan nan, mun shaida zaɓe ba tare da rikici, amfani da makamai ko magudi ba a Kano. Wannan cigaba ya dace da manufofinmu na fifita Kano.
Zamanin kashe-kashe, jikkata jama’a da hana su kaɗa ƙuri’a ya zo ƙarshe.”
Ya ƙara da cewa nasarar gudanar da zaɓen cikin lumana na nuna cewa Jihar Kano a shirye take ta rungumi siyasar da ta dogara da tattaunawa, haƙuri da mutunta ƙa’idodin dimokuraɗiyya.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko ga tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko addini ba.
Haka kuma ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin zaɓe da na tsaro domin tabbatar da cewa duk wasu zaɓuka a gaba sun kasance masu gaskiya, adalci da zaman lafiya.

