Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rantsar da sabbin kwamishinoni guda bakwai da ya nada a watan Disambar 2024 da ya gabata.
Kwamishinan shari’a na Kano Kuma babban lauyan jihar, Barista Haruna Isa Dederi shine ya rantsar da sabbin kwamishinonin 7 tare da sauran masu baiwa gwamna shawara.
Haka Kuma kwamishinan na shari’a Barista Dederi ya jagoranci rantsar da masu baiwa gwamna Yusuf shawara guda 12 daga cikin guda 17 da aka nada a kunshin gwamnatin Kano
TST Hausa ta rawaito cewa tuni gwamna Yusuf ya tura sabbin kwamishinonin zuwa ma’aikatun da aka tanadar musu.
Gwamnan ya amince da hakan ne a fadar gwamnatin jihar Kano ranar litinin 6 ga watan Janairun 2025.
Sabbin Kwamishinonin da gwamna Yusuf ya jagoranci rantsarwa kuma ya amince da basu ma’aikatun da zasu jagoranta sun hada da :
1.Alhaji Shehu Wada Sagagi, da zai kula da ma’aikatar
2.Kwamared Ibrahim Abdullahi Waya, an turashi ma’aikatar
3.Dr.Dahir Muhammad Hashim an amince ya rike ma’aikatar
4.Abdulkadir Abdussalam, shi kuma gwamna Yusuf ya amince ya rike ma’aikatar
5.Dr. Isma’ila Aliyu Dan Maraya ,an turashi ma’aikatar
6.Dr.Gaddafi Sani Yakubu,an turashi ma’aikatar
7.Dr.Nura Iro Ma’aji , ma’aikatar gwamna Abba ya amince ya rike
Sabbin Kwamishinonin zasu fara zaman majalisar zartaswa na nan gaba da za’a sanar.
TST Hausa ta gano cewa a ranar Talata 18 ga watan Disamba na shekarar 2024 data gabata ne majalisar dokokin Kano ta amince da mutane 7 din da gwamna Abba Yusuf ya tura mata dan a tantancesu a kuma amince masa ya nada su kwamishinoni,bayan garambawul da yayi a cikin majalisar zartaswarsa.
Gwamna Yusuf ya taya kwamishinonin murna tare bukatarsu da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, tare da rungumar kowa a gwamnati dan amfana da romon Demokaradiyya.
Ya kuma neme su da su rike gaskiya da amana.

