Kungiyar tsaffin yan sandan Najeriya NUP reshen Kano,da suka ajiye aiki sunyi barazanar fara yajin cin abinci domin matsawa gwamnatin tarayya da hukumar kula da fanshon yan sanda su biyasu hakkokinsu .
Sakataren Kungiyar tsaffin yan sandan Najeriya NUP reshen Kano Kwamared SP Sa’idu Garba (Mai ritayar )shine ya tabbatar da hakan a zantawarsa da TST Hausa a yammacin Laraba.
Yace ya zama wajibi su fara yajin cin abincin saboda a baya sunyi duk abinda ya dace ciki harda zanga zangar lumana a majalisar tarayya ta kasa dan biyansu hakkokinsu na giratuti.
Ya shaida cewa Sama da shekara 10 suke bibiyar hakkokinsu amma har yanzu Shuru.
Saidai yace a baya ,saboda zanga zangar lumana da sukayi ,yasa majalisar dattawa tayi karatu na daya dana biyu dan ciresu daga Hukumar kula da haraji ta kasa (PenCom) da take rike musu kudadensu.
SP Sa’idu Garba yace a duk wata abinda ake bashi bai wuce naira dubu 30 ba .
Nayi ritaya daga aikin dan sanda a shekarar 2007 ga tarin iyali amma abinda ake bani bai taka kara ya karya ba;Inji tsohon dan sandan
Yace dukanin shugabaninmu sunki cewa komai akan zalincin da ake mana dan gudun kada su rasa aikinsu .
Ko a watan Oktoban da ya gabata saida Jami’an ‘yan sanda da suka yi ritaya suka koka kan rashin daidaiton kudaden fansho da ke tsakanin su da takwarorinsu na sojoji, inda suka zargi gwamnati da yin sakaci.
A ranar 29 ga watan Nuwamba da ya gabata tsaffin yan sandan a Najeriya sun nemi majalisar tarayya da ta ciresu daga tsarin bayar da gudunmuwar fansho na CPS.
An kafa hukumar ta kula da tattara kudaden tsaffin yan sanda (PenCom) a shekarar 2004 .

