Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da aikin kashe Ɓeraye a karamar hukumar Garun Malam domin dakile yaduwar cutar Lassa.
Kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, sanarwa da aka turawa TST Hausa.
Kwamishinan yace ya zama dole gwamnati ta dauki wannan mataki na gaggawa domin kare lafiyar al’umma, ganin yadda aka tabbatar da bullar cutar Lassa a Garun Malam, wacce ta yi sanadin rasuwar wata mata a Asibitin Aminu Kano makon da ya gabata.
Kwamishinan ya bayyana cewa tuni aka killace duk wadanda sukayi mu’amala da mamaciyar, ciki har da mai gidanta da kuma jami’an lafiyar da suka kula da ita lokacin da aka kaita asibiti.
TST Hausa ta gano cewa binciken da aka gudanar ya tabbatar da mijin marigayiyar da daya daga cikin yaranta sun kamu da cutar ta Lassa Garum Malam.
Dr. Labaran ya jaddada cewa kashe Ɓerayen da ke yankin da abin ya shafa wani muhimmin mataki ne na dakile yaduwar cutar, kasancewar Ɓeraye na daga cikin manyan hanyoyin yada cutar Lassa.
Gwamnatin ta kuma ja hankalin mafarauta da su guji farautar Ɓeraye, da kuma daukar matakan kariya domin hana yaduwar cutar daga jikinsu zuwa ga mutane.
Kwamishinan ya shawarci jama’a da su rika hanzarin sanar da jami’an lafiya mafi kusa idan suna da wani zargin cutar Lassa.
Haka zalika, ya bukaci jami’an lafiya da su dauki matakan kariya yayin da suke kula da masu fama da cutar, domin kauce wa yada ta.

